Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gadar Gilashi Ta Farko A Duniya


Gadar Gilashi a China
Gadar Gilashi a China

A karon farko kasar China, an bude wata sabuwar gada wadda aka yita da Gilas, gadar na da tsawon mita dari tara da tamanin 980 Ft. Tana nesa da kasa da mitoci dari shida 600, kusan kamar ace tsawon gidan bene mai hawa ashirin 20.

An sakawa gadar suna “Gadar mazan jiya” wadda take cikin harabar yankin da baki 'yan-yawon bude ido ke zuwa shakatawa, da ke yankin kudancin kasar China. A tabakin wani ma’aikacin kamfanin da sukayi aikin gadar, ya tabbatar da cewar gilashin da akayi amfani da shi yana da kaurin fiye da kashi ashirin da biyar 25% na sauran gilas.

Ya kuma tabbatar da amincin gilas din, da jaddada inganci da gadar, kana anyi amfani da karfe mai matukar mahimanci wajen karawa gadar karfi. Dubun dubatan mutane 'yan yawon shakatawa da 'yan kasar sunyi tururuwa wajen tafiya akan gadar, bayan suna hangen kasa. Wasu daga cikin mutane basu iya tafiya a tsaye ba, don tsoron da jiri da suke gani.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG