Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Rashin Amsa Gayyatar Buki Sai Tara Daloli?


Amarya da Ango
Amarya da Ango

Ana iya cewa kowace kasa, kabila, nada irin al’adun su daban-daban, wani abu a wata kasa ko kabila kan zama wani abun mamaki, ko abun ki ga wasu. A kasar Amurka, ana mutunta gayyata musamman ma idan ta buki ko suna ce.

Sabo da tsabar mutunta gayyata, wata mata mai suna Jessica Baker, da mijin ta a jihar Minnesota, basu samu zuwa wani buki da aka gayyace su ba, akan dalilin cewar mai rikon musu ‘yar su, baza ta samu damar rike masu ‘yar ba, don haka basu samu damar zuwa ba, domin kuwa a cikin katin gayyatar an ce kada mutun yazo da yara.

Bisa wannan dalilin na rashin zuwa bukin da yara, yasa basu da yadda za suyi da ‘yar ta su. Bayan kwanaki da gama bukin, sai kawai a’ka aiko masu da cewar an cisu tara, domin basu samu zuwa bukin da aka gayyace su ba, domin kuwa Amarya da Ango sun sa sunan ta da na mijinta akan cewar za suzo. Sai basu zoba, don haka anyi abinci da su, kuma basu zoba, don haka sai su biya kudin abincin da aka ajiye da su.

A jikin katin da aka aiko musu an bukace su da su biya kudi dallar Amurka $75 dai-dai da naira dubu goma sha biyar 15,000. An kuma rubuta cewar “Da kun san baza ku zo bukin ba, ai ko da sakon waya “text” kun aiko, sai mu cire ku daga cikin bakin mu.”

Ita dai Jessica, tace bata da wani tunani na biyan wannan tarar, domin kuwa bata san dacewar baza, su samu damar zuwa bukin ba har sai ranar, don kuwa a wannan ranar ne mai rikon ‘yar su take gaya musu cewar bazata samu damaba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG