Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saurayi Da Budurwa Sunyi Tadi Da Yafi Kowanne Tsada A Duniya


Verizon Earns
Verizon Earns

Sau da dama mutane kanyi kuka cewar an sace musu kudi, a layin wayar su batare da sunyi wani abu da wayar ba. Wani saurayi da budurwa Mr. Ken Slusher, suna kokarin sayan wani gida, sai aka duba tarihin yadda suke kashe kudi. Ana bincikawa sai aka gano cewar ana binsu kudin waya da basu biya ba na tsawon watanni goma da suka kai dallar Amurka milliyan biyu da dubu dari daya da hamsin da shida da dari biyar da casa’in da uku da cent sittin da hudu $2,156,593.64.

Kudin za suyi dai-dai da naira milliyan dari hudu da talatin da daya, da dubu dari uku da sha takwas, da dari shida =N=431,318,600. A zahiran ce wannan kudin sun fi, adadin kudin da wasu kananan hukumomi da yawa kan karba a matsayin kudin gudanarwa na kananan hukumomi daga gwamnatin tarayya a watannin masu dama.

A tabakin Mr. Ken, yace wannan wani abun almara ne! Rahorannin na nuni da cewar sun biya kudin gidan kasa ba bashi, amma akwai alamun kamfanin Verizon, suna iya kwace gidan daga hannun su, don maye gurbin kudin da suke bin su na wayar da sukayi basu biya ba na kimanin tsawon watannin goma.

Duk dai da cewar kamfanin ya nuna cewar, wannan wani kuskure ne daga bangaren su, kuma suna kokarin wajen gyara hakan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG