Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wata Sabuwar Duniya Cike Da Tsirran Ganyen Wiwi


Duniyar wata
Duniyar wata

Hukumar bincike a sararin samaniya “NASA” sun bayyanar da ganin wata sabuwar duniya, wadda ke cike da tsirran ganyen wiwi. Wannan binciken ya bama duk daukacin masu gudanar da binciken mamaki, sun ce duniyar X637Z-43 an gano ta ne a lokacin da akayi amfani da na’urar hange ta hukumar.

Sun kara da cewar wannan na iya zama daya daga cikin irin wasu duniyoyi, da basu bayyana ba, a cewar masana na NASA, sun kuma iya gano cewar, akwai wadataciyar iskar gas, a duniyar wanda dan’adam kan iya rayuwa a wajen.

Masanan dai sun kara da cewar, samun ganyen wiwi a nahiyar na iya zama wani abu da zai sa mutane, su zurfafa bincike a kan ganyen. A tabakin Mr. David Charbonneau, malami a tsangayar binciken rayuwar wata da taurari, na jami'ar Harvard, yace mafi aksarin matasa suna son ganyen wiwi, don haka akwai bukatar matasa su tashi tsaye wajen bincike, don gano alfanun ganyen ba kawai su dinga shan shi ba, wanda har zai kauda musu da tunanin suba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG