Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Zama Na Haddasar Da Cutar Hannta


Hanta
Hanta

A wani bincike da aka gudanar, a jami’ar Newcastle ta kasar Birtaniya, da ke nuni da cewar yawan zama a waje daya, na daga cikin abubuwa da ke haddasar da cutar Hannta, baya ga kwan-kwadar barasa.

A cewar farfesa Michael Trenell, mutane da ke zama a waje daya, na awowi goma ko fiye a rana. Na da kashi tara 9% na hatsarin iya kamuwa da cutar ciwon hannta cikin gaggawa. Don haka akwai bukatar muta ne suyi tafiya, mai kwatan-kwacin taku dubu goma 10,000 a rana, ko kuwa suyi aikin motsa jiki na kimanin mintoci dari da hamsun 150 a sati.

Wannan zai taimaka matuka wajen samun ingatacciyar lafiya ga al’uma, musamman ma idan matasa zasu dauki wannan, ya zama cikin dabi’un sun a yau da kullun. Yin hakan zai basu damar idan tsufa ya zo musu su, su zamo masu karfi da amfani ga kansu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG