Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Bukin Haihuwar Karyar 9/11


Bukin haihuwar Karya
Bukin haihuwar Karya

A kasar Amurka, ana bama dabbobi matukar kulawa ta musamman, a jiya ne aka karrama wata karya mai suna Bretagne. A lokacin da ake bukin cikar ta shekaru goma sha shida 16, wanda kuma yayi dai-dai da, ranar da ake tunawa da mutanen da suka rasa rayukan su, a lokacin da aka kai harin ta’addanci a dogayen tagwayen ginanuwa dake babban birnin New York.

Wannan karyar dai tana daga cikin karnukan da akayi amfani da su, a lokacin da ake kokarin gano mutane da suke cikin kasa, da kuma gawar wadanda suka rasa rayukan su. Ita dai wannan karyar itace kawai wadda ta rayu tun bayan wannan abun da ya faru kimanin shekaru goma sha hudu 14 ke nan.

A lokacin karrama wannan karyar, an saukar da mai karyar Denise Corliss, da karyar, a Otel mai tsada kana kuma an bama karyar kyaututuka da dama, kamar yadda akema yara bukin cika shekara a nan kasar Amurka, kuma an nuna hoton wannan karyar a babban talabijin na kan titi a cikin kwaryar garin New York.

An karrama karyar, da karramawa mafi girma da “Kashi”, a matsayin makulin garin New York. Wanda bisa ga al’ada idan akayi bakon kunya, kamar shugaban wata kasa idan yazo, akan bashi wannan a matsayin karrama bako a garin da yafi komi. A lokacin da aka nuna karyar a talabijin mutane da dama sunyi kuka don tunawa da wannan mumunan ranar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG