Ga duk namiji mai neman budurwa ko mace mai neman saurayi. A kwai abubuwa guda uku 3, da yakamata a kaurace ma, idan har da gaske a na bukatar samun daya daga ciki na kwarai batare da yaudara ba.
Abu na farko shine, duka tsakanin maza da mata, kowanne ya san abun da yake so, da kuma abun da yake son saurayi/budurwa su zama. Tare da mantawa da abun da kuke son zama. Sau da dama, mutane kan sama kan su dogayen buri masu yawa, da cewar yarinya ko saurayi sai suna da wadannan abubuwan, sannan zan saurare su. A lokkuta da dama akan ce idan bashi da ko batada kwalin digiri, ko yana daukar albashi kaza, ko kuwa baban ta mai kudine, koma ‘yar gayu mai kwalisa, sai yana da mota irin wace, ko kaji ance ai ni sai fara mai gashi, da dai ire-iren wadannan abubuwan.
To babu shakka wadannan abubuwan baza su bama dukkan masu wadannan zabin damar iya tsaya waje daya don zaben nagari ba. Da yawa ba’a duba wai meya sa nake son wane, ko kuwa mai rayuwa zata zama a gaba idan mukayi aure da irin wannan mijin ko matar?
Abu na biyu, kada kowannen yayi kokarin barin burin sa ya rinjayi hankalin shi da tunanin, a wasu lokkuta mutane kan manta cewar ba dubarar, wayo, ko yawan ilimin mutun ke bashi abu ba, mafi akasarin wannan zamanin za’aga cewar mata da maza, sukanyi tunanin cewar idan na aure shi saboda yana da kwalin digiri zamuyi kudi da wuri, shi kuwa zai ga cewar ai da na aureta iyayen ta suna da kudi muma zamuyi kudi nan da nan.
Abu na uku, wasu lokkuta mutane sun san abun da basu so, amma basu san abun da suke so ba. Abun nufi a nan shine matasa kan makance da soyayya, basa duba abubuwan da suka faru a baya, na cin amana da ya faru da kai/ke koma ace wani labarin cin amana da ya faru da aboki/kawa don ya zama darasi. Wanda kuma kamata yayi a ce matasa su dinga sara suna duban bakin gatari, a duk lokacin da akayi maganar soyayya. A sanadiyar rashin duba wadannan abubuwa ukun, matsa kan shiga halin danasani a wajen neman abokan rayuwa.