Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsatsaku Cikin Rafi Babbar Hatsari Ga Rayuwa


Mutuwa ba sabuwar abu bace amma mutuwa irin ta matashi Michael John Riley, dan shekaru goma sha hudu 14, abun tambaya ce. Dubun dubatan mutane za suce wai menene abun mamaki da mutuwar wannan matashin? A ranar 13 ga watan Augusta, wanna matashin su na cikin rafi su na wanka, sai wata tsutsar ruwa da ake kira “Matsattsaku” ta shige ma wannan matashin hanci.

Ita dai wanna tsusar takan shiga jikin dana dam wanada kuma idan har tashiga ta hancin mutun sai ta shiga kwakwalwar mutun don yimasa barna, wanna shine abun da ya samu wanna matashi a yayin da suke wanna wasan a cikin ruwa. Tun bayan wanna yaron ya fara rashin lafiya kwanaki kadan ya rasu.

Bincike ya nuna cewar mutane biyu ne kawai aka taba samu sun kamu da wanna cutar kuma suka rayu. Mafi akasarin wadanda suka kamu da wanna cutar sukan mutu cikin karamin lokaci. Ana jawo hankali matasa da su guji shiga cikin ruwa wanda yake dauke da cututuka domin kuwa ta haka ne za’a iya kamuwa da wanna cutar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG