Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ai Ko Baba Da Babanshi Bincike A Tafin Hannu


Shafin yanar gizo
Shafin yanar gizo

Ai ko baba da babanshi, a lokkuta da dama, mafi akasarin mutane a duniya kanyi amfani da shafin Google, wajen bincike kowane iri a wanna zamanin. Yawan ci idan aka sa sunan wani mutu a wanna shafin na google, za’a iya samun takai taccen bayani ko labarin mutun, wanda harma idan wanna mutumin yana da wani shafin zumunta na yanar gizo, du kana iya ganin su ta nan.

An kara samar da wasu shafufukan wadanda zasu bama mutun bayanai masu dama, danga ne da mutane a fadin duniya. Wani abun la’akari dashi a nan shine, wadanna shafufukan suna iya nuna maka wasu sirikan mutun, ko ace zasu nuna maka fiye da abun da shafin google zai nuna maka, a dangane da wanna mutumin da ake nema.

Domin kuwa wanna shafin zai nuna maka idan mutun yataba yin laifi ko cin amana, sata, da dai duk wani abu da zai sa kada wani abu ya hada wata hulda da mutun. Ko kuwa ace idan mutun yana neman wata budurwa, zai iya sa sunan ta don ganin duk irin abubuwan da ta tabayi a rayuwar ta. Idan kuwa mutun yayi maka karya, zaka iya gane gaskiya idan kasa sunan shi a wanna shafin, kai koda ma mutun ya karya dokar titi duk kana iya ganin rin abubuwan da mutun ya aikatar a tsawon rayuwar shi. Sababbin shafufukan sune “innovative new website ko instant checkmate” don kara fadada bincike sai matasa ayi amfani da wanna damar yadda yakamata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG