Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dadin Soyayya Sai Da Saurayi Dan-Karya


Samartaka ds karya
Samartaka ds karya

Wai me yasa ‘yan mata basu son gaskiya? Na kasan ce tsawon shekaru shida ina soyayya da tsohon saurayina, yakan kalleni yace bani da kyau, nacika kiba, bani da hali mai kyau. Wasu lokkuta ma har ya kan kai ga duka na.

Sai ka wai yau nawayi gari nasamu wani sabon saurayi, ko da yaushe sai ya kalle fuska ta yace nafi kowace mace kyau a doron duniya. Ni kuwa bana iyace mishi komai, domin kuwa inaganin kamar ba da gaske yake ba.

Amma abun mamaki a nan shine wai da gaske yake kuwa? A kowane lokaci nakan tambayi kaina, amma fa nike gaba da shi a wajen aiki, to ko wanna yana daga cikin dalilin da yasa yake cemun ina da kyau?

To yazan billo ma wanna matsalar, don kada ta zama babbar matsala a rayuwa ta, a nan gaba? Hakan kan iya samun kowace mace. To menene shawarar ku ga maza ko mata masu irin wanna halayen.

Kuje shafin mun na dandalinvoa/Faceebook.com don muhawara a kan wanna matsalar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG