WASHINGTON DC, —
A kasashe kamar su Amurka, Canada, da suke yankin Arewacin duniya. Bisa ga al’ada a nan kasar Amurka, duk ranakun goma sha biyu 12, goma sha uku, da goma sha hudu 14 na Austa. Miliyoyin mutane kanyi bacci da rana kana su tashi tsakar dare domin ganin wata halittar Allah.
A duk dare na waddannan kwanakin a watan Augusta na kowace shekara, miliyoyin turawa kan fito tsakar dare su kalli sararin samaniya da Allah, ke kawata ta da biliyoyin ruwan Taurari, wanda har suke boye hasken wata.
A na dai kiran wanna ruwan taurarin “Perseid Meteor Shower” a turance. Wannan wani abun ban sha’awa ne, don kuwa wata baiwa ce ta Allah. Da safiya kuma hasken rana kan fito a kurraren lokaci ba kamar yadda hasken yasaba fitowa ba.