Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Amosanin Jini Bata Hana Rayuwar Yau da Kullun


Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo
Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo

Kowane mahaluki na samun jarabawa daban daban a rayuwa, babban muhimmin abu a nan shine, yakamata ace kowace irin jarabawa mutun yasamu kanshi a ciki to yakamata ya godema Allah, kuma kada yayi kasa a gwiwa. Malama Zahra’u Sani Abdullahi, wata baiwar Allah ce, mai fama da cutar amosanin jini, wanda wannan wata cuta ce wadda take hana mutane more rayuwar su, amma duk da wannan cutar bata maida kanta baya ba, ta tashi tsaye wajen neman zama daidaito da sauran mutane.

Duk da irin hali da tasamu kanta na ciwon wanda wasu lokkuta takan yi kamar bazata rayu ba, amma ta iya kokarin komawa makaranta, wanda har ta samu ta gama karatun ta na jami’a, wanda ma gashi yanzu ta na aiki.

Duk da haka batabari ta zama wadda za’a dinga taima kama a kowane lokaci ba, tana nata kokarin wajen ganin ta taimaka ma masu irin wannan cuta, da shawarwarin yadda yakamata su bi wajen magance ita wannan cutar, musamman idan gari na da danshi ko buji, to ya kamata mutane su guji fita cikin irin wannan yanayi, don tahaka ciwon na iya tashi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG