Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Ingantacciyar Rayuwa ga Matashi Mara Kishi


Matasa
Matasa

Mukhtari Ibrahim, wani matashi ne wanda yake kokarin dogaro da kanshi, ta hanyar samar ma kanshi sana’a wada yake yi bayan ya dawo daga makaranta. Yana siyar da lemun kwalba da ruwa, wanda dasu ne ya dogara, kuma yake taimakama kansa da iyayenshi.

Ita dai wanna sana’ar tashi bata hanashi karatuba ko gudanar da ma’amar shi ta yau da kullun. Duk da cewar yakan fuskanci wasu matsaloli amma bai sa yayi kasa a gwiwa ba, wajen dagewa da neman yadda zai iya zama wani abu a rayuwa batare da ya jira gwamnati ko wani yayi mishi ba.

Yayi kira ga matasa da su tashi tsaye wajen neman nasu na kansu, dakuma kokarin taimakama duk wadanna ke da bukatar taimako, don ta irin wannan dogaro da kai ne kawai wasu zasu samu kwarin gwiwan neman nasu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG