An yaba da wani sabon batir da ka iya samar da makamashi na lokaci mai tsawo, kuma a farashi mai rahusa a rabin kudin da ake kashewa a yanzu, ana zuga batirin a zaman juyin juya halin makamashin da zai maye gurbin hanyoyin samun wutar lantarki a Nahiyar Afrika.
Wani kamfanin fasaha da cibiyarsa ke jihar Caliornia nan Amurka ne ya kirkiro da wanna batir. Batirin yana iya adana makamashin baiwa duk gida karfin lantarki na tsawon awowi biyar.
Shugaban kamfanin mai suna Elon Musk, yace kamfanin yayi la’akari da Afirka alokacin da ya kirkiro batirin da za’a iya makalawa a bango don samun makamashin lantarki. Kamar yadda wayoyin hannu a Afirka suka taimaka wajen baiwa Nahiyar sukunin shiga yanar gizo, haka zalika shi wannan batirin zai iya baiwa gida ko gurin sana’a karfin lantarki wanda hakan zai taimakawa nahiyar Afirka wajen samun cigaba sosai a fannin samun wutar lantarki.
Kamfanin yayi alkawarin fitar da fasahar da ya kirkiro ga kowa domin amfanin jama’a, yana kuma karfafawa sauran kamfanoni guiwa domin su kirkiro irin nasu baturin.
Batirin mai karfin kilowatt goma yana da tsada idan akayi la’akari da yadda za’a saye shi kan dalar Amurka $3,500 amma ana sa ran farashin zai sauka nan da wasu shekaru idan wasu kamfanonin suka kirkiro nasu samfurin.
Nahiyar Afirka tafi kowacce nahiya wahalar samun isasshen wutar lantarki a duniya. Kwata kwata karfin wutar lantarki da ake samarwa a kasashen bakar fata na Afirka, bai shige abinda kasar Spain take samarwa ita kadai ba, kuma rabin dukkan karfin lantarki yana kasar Afirka ta Kudu.
Amma kila abu mafi muhimmanci shine Afirka zata iya zama cibiyar samar da makamashi daga kafofin da aka iya sabuntawa.
Nahiyar Afirka tafi ko ina a duniya albarkatun hanyoyin samar da wutar lantarki ta hasken rana ko karfin iska a saboda makekiyar hamadar sahara da iska mai karfin gaske a gabobin tekun nahiyar.