A bayan muhawara mai zafi, Majalisar Kasa ta yanke shawarar kyale hukumar zaben Najeiya ta INEC da ta gudanar da zabe kamar yadda ta shirya a bayan ta tuntubi jami'an tsaron kasar.
Rahotanni sun bayyana da dama dake nuna cewa sojojin Najeriya ne suka nemi a jinkirta zaben da watanni biyu bisa hujjar cewa su na bukatar karin wannan lokacin domin shawo kan matsalar Boko Haram.
Amma majalsar, wadda aikinta bayar da shawara ce kawai, ta ce a bar hukumar INEC ta yi abinda ta ga ya dace, a bayan da shugabanta, Farfesa Attahiru Jega, ya nace a kan cewa sun shirya ma zaben.
Kafin nan, an yi zanga-zanga a cikin Abuja domin nuna rashin yarda da duk wani matakin jinkirta zaben, matakin da wasu ke ganin cewa yunkuri ne da jam'iyya mai mulki ta PDP keyi na ci gaba da zama kan karagar mulki.