Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salman bin Abdul'aziz al-Sa'ud Ya Zamo Sarkin Sa'udiyya..Ya Nada Muqrin A Zaman Yarima Mai Jiran Gado


Sarki Salman bin Abdulaziz na Sa'udiyya
Sarki Salman bin Abdulaziz na Sa'udiyya

Yarima mai jiran gado na Sa'udiyya, Salman bin Abdul'aziz al-Sa'ud, ya zamo sabon sarkin Sa'udiyya da asubahin nan a bayan rasuwar Sarki Abdullahi da karfe 1 na dare agogon Saudi.

An haifi Sarki Salman ran 31 ga watan Disambar 1935. An ce shi ne da na 25 na mutumin da ya kafa wannan gidan sarauta ta Sa'udiyya, watau Abdul'aziz Ibn Sa'ud. Mahaifiyarsa ita ce Hassa al Sudairi.

Sarki Salman yayi karatu a Makarantar 'Ya'Yan Sarki dake Riyadh, inda ya karanta Addini da kuma Kimiyyar Zamani.

Salman ya fara aikin mulki tun yana saurayi mai shekaru 19 da haihuwa. Mahaifinsa ya nada shi sarkin Riyadh a ranar 17 Maris 1954.

A ranar 4 Fabrairu 1963, an nada Salman a zaman gwamnan Riyadh, kuma ya shafe shekaru kusan hamsin yana rike da wannan mukamin.

A ranar 5 Nuwamba, 2011, Yarima Salman ya zamo ministan tsaro na Sa'udiyya, a bayan rasuwar dan'uwansa marigayi Yarima mai jiran gado Sultan.

A ranar 18 Yunin 2012, an nada Salman a matsayin Yarima Mai Jiran Gadon sarautar Sa'udiyya a bayan rasuwar mai rike da wannan mukami a lokacin, Nayef bin Abdul'aziz. Haka kuma a lokacin aka nada shi mukaddashin firayim ministan Sa'udiyya.

Yau Jumma'a da asuba kuma, aka ayyana shi a zaman Sabon Sarkin Sa'udiyya.

XS
SM
MD
LG