Masana da masu kula da dakin ajiye kayayyakin tarihi na Masar sun ce an 'karon da aka yi amfani da shi domin mayarda gemu mai launin shudi da gwal na mutum mutumin da aka binne wani sanannen fir’auna mai suna Tutankhamun a ciki da shi ya lalata wani gefensa.
Mutum mutumin ya lalace a bayan da aka ture shi bisa kuskure lokacin da ake kokarin wanke shi a dakin dake al-Qahira.
Sai dai kuma wannan 'karon an ce ya latata wannan kayan tarihin.
Wannan dakin kayan tarihi na daya daga cikin wuraren da ‘yan yawon shakatawa da bude ido suka fi yawan zuwa a al-Qahira, inda aka baza kayayyakin tarihi masu yawa da Masar ta yi suna kansu tun na zamanin jahiliyya.
Wannan mutum mutumin da aka rufe akwatin gawar Fir’auna Tutankhamun da shi, fiye da shekaru dubu 3 da suka shige, yana daya daga cikin abubuwan da mutane suka fi zuwa kallo.
Wasu ma’aikatan dakin ajiye kayan tarihin sun ce ba ayi amfani da irin 'karon da ya dace wajen sake mayar da gemun mutum mutumin ba, kuma ba za a iya sauyawa ko gyara barnar da 'karon yayi a jikin wannan gemun na akwatin gawar fir’auna Tutankhamun ba.
Aka ce 'karon ya bushe a jikin fuskar mutum mutumin, kuma da aka yi kokarin gogewa sai ya haddasa zane zane a jikin fuskar.