A karon farko China tayi bikin tunawa da zagayowa da kuma cikar sheakaru 77 da ranar kisan kare dangi da ake kira Nanjing Massacre, a zamanin da sojojin Japan da suka mamaye kasar a bahasin da Beijing ta bayar, suka kashe farar hula da sojoji da basu dauke da makamai da ake ake kiyasin yawansu ya kai dubui dari uku, suka yi fyade ga mata kimanin dubu ashirin.
A cikin ajwabinda ya gabatar yau Asabar a Nanjing, tsohuwar fadar China, shugaba Si Jinping ya gayawa wadanda suka hallara da suka hada da sojoji da kuma wadanda suka tsira daga harin a watan disemban 1937 da kuma dalibai, cewa makasudin tunawa da wannan rana shine "karfafa burin da kuma hankoron ko wani Bil'adama na ganin an mutunta zaman lafiya, maimakon zakalkalewa kan yada akidar gaba.