WASHINGTON, DC —
Kasa da mako guda a bayan da ya fice daga cikin jam'iyyar PDP, sanata Abubakar Atiku Bagudu ya zamo dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a Jihar Kebbi.
A bayan da aka shafe kwanaki biyu da rabi ana gudanar da zaben fitar da gwanin, sanata Atiku Bagudu ya doke sauran mutane 4 da suka yi takarar da shi da kuri'u masu yawan gaske.
Sanata Bagudu yace ba zai fuskanci babban kalubale a babban zaben da za a yi ba a saboda a cewarsa, yanzu sun farga cewa jam'iyyar PDP ba zata iya biyan muradun al'ummar jihar ba.
Sai dai kuma, sauran wadanda suka yi takara da shi din sun koka a kan cewa an yi magudi, kuma tun farko an shirya wannan zaben ne ta yadda zai fito a zaman dan takara.