Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi Na Biyu, ya roki jama'a da a rika kai zuciya nesa idan wani abu na masifa ya faru, yana mai cewa ba a tinkarar masifa da fushi, sai dai da hakuri da kuma dangana ga Ubangiji.
A jawabin da yayi lokacin da yake tarbar mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo, wanda ya kai ziyarar jaje a fadarsa, Sarki Sanusi ya ce su a Kano, sun yarda cewa babu wata masifar da zata fada musu sai abinda Allah Ya rubuta musu.
Yace mutanen da aka hallaka, "'ya'yanmu ne, 'yan'uwanmu ne, wadanda ba su aikata wani laifi ba, sun je wurin ibada ne." Yace ana yi wa mutanen kyakkyawan zaton shahada, kuma Allah Ya karbi shahadarsu.
Ya roki jama'a da su guji jita-jita su kuma hada kai da jami'an tsaro wajen samun kwanciyar hankali.
Sarkin na Kano yace lallai ne shugabanni su bincika a ga yaya aka yi wannan abu ya faru, su wanene suka aikata shi, kuma wane irin hukumci ya kamata ayi musu? Haka kuma, mutane da kasashen da abin ya shafa, wasu matakai za a dauka domin taimaka musu.
Sarki Muhammad Sanusi ya godewa jami'an tsaro dake Kano a saboda irin kokarin da suke yi, tare da yin kiran a karfafa matakan tsaro a fadin kasa baki daya.