A wani bayani da aka fidda yau jumma’ daga kwamitin da arewacin kasar ta kafa akan tabbatarda zaman lafiya tsakanin arewa da kudancin kasar, kwamitin ya yi kashedin cewa sa takunkumi tamkar yin yakine da Koriya ta Arewa.
Sanarwar kuma ta yi barazanar kawo karshen duk wata tattaunawa akan dena yin makaman nikiliya.
Rana larabar da ta wuce, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harba rokar da Koriya ta Arewa ta yi a watan disambar da ta gabata, ta bayyana wannan a matsayin saba wa takunkumin da ya hana yin makami mai lizami da kuma na’urar nukiliya.
Kan hakan ne, Koriya ta Arewa ta maido da murtani a jiya cewa zata yi gwajin makaman nukiliya zata kuma kara harba wasu rokokin.