A cikin sanarwar da ta bada ta hannun kampaninta na dillacin labaru, Koriya ta Arewa tace zata yi wannan ne don kawai ta bata wa babbar abokiyar gabata, Amurka, rai.
Sai dai sanarwar da Hukumar tsaro ta kasar ta bada, ba tace ga lokacinda Koriya zata aiwatarda wadanan gwaje-gwajen ba.
Amma an san cewa duk wannan barazanar ta Korea ta Arewa tana zuwa ne bayan kuri’ar da dukkan kasashen dake cikin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya suka jefa ne, inda suka zartad da kudurin la’antar Koriya din akan rokokin da ta harba a watan Disambar da ya gabata, wanda ya saba wa kudurorin da aka sha yankewa da suka haramta mata kera duk wasu makamai ko fasahu masu alaka da nukiliya.