Rahotanni daga kasar Iraqi na cewa hare-haren boma-bomai a ciki da zagayen birnin Bagadaza sun kashe mutane akalla goma sha shida.
Harin boma-boman na yau Talata sun hada harda wanda aka kaiwa sansanin sojin Iraqi dake Taji mai tazarar kilomita 25 Arewa da birnin Bagadaza.Mutane shida ne suka rasa rayukansu sannan akalla mutane 20 suka jikkata.
Wani Tashin bom da aka nasa mota kuma ya tashi, mutane biyar suka halaka cikinsu harda soja biyu a kusa da wurin binciken ababan hawa kan titin Mahmudiyah, kudu da birnin Bagadaza. Bom na uku kuma ya tashi ne a unguwannin Shula cikin birnin bagadaza, mutane biyar ne suka halaka.
Babu wata kungiyar da tace ita keda alhakin kai wadannan hare-hare.