Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kano Ta Hana Daukar Mutane Akan Babur


Hoton cikin birnin Kano kennan.
Hoton cikin birnin Kano kennan.
Gwamnatin jihar Kano ta hana daukar mutane akan babur daga ran Alhamis, 24 ga wannan wata a cikin birnin Kano, da kananan hukumomin kewaye.

A jawabin da mataimakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi Talatan nan, dan Jam'iyyar Peoples Democratic Party yace hakan zai taimaka wajen yi wa bubura rejista da kuma takalar rashin tsaro dake damun birnin Kano.

Wakilin Muryar Amurka, Muhammad Salisu Rabi'u ya bada rahoton korafin da Kungiyar 'Yan Achaba na jihar Kano keyi na rashin ayyukanyi, da kuma rashin cika alkawari da gwamnatin jihar Kano tayi musu.

Shugaban Kungiyar 'Yan Achaba na jihar Kano, Alhaji Muhammad Sani Hassan ya gayawa wakilinmu cewa gwamnatin ta sanar dasu akan wannan batu, kuma ta shafa wa idannunta kwalli, na cewa ba'a yarda akai yara makaranta ba, ko mara lafiya asibiti akan babur. Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar tayi wa 'yan achaba alkawarin motocin bus dari biyu domin sana'a tun watan Yuni, amma zuwa yanzu, guda ishirin kawai aka basu. Ya kira gwamnati da ta sake duban wannan doka.

Sana'ar achaba dai, na daya daga cikin hanyoyin samun kudi a Najeria, amma jihohi da dama sun hana yin ta. A jihar Kano, Hukumar Kudaden Shiga na Cikin Gida ta ce tayi rejistan 'yan achaba guda miliyan daya da dubu dari takwas. Wannan kiyasi dai bai hada da mutanen dake amfani da baburansu ba, domin harkokin yau da kullum.

Wakilinmu, Muhammad Salisu Rabi'u ya gana da mutane a cikin gari domin jin yadda suka karbi wannan mataki. Wani dan achaba, mai suna Muhammad Yusuf yace babban kalubalen da yake fuskanta yanzu, shine samun aikin yi.

Sana'ar achaba a jihar Kano dai, anyi shekaru 30 ana yi amma a baya-bayannan, 'yan bindiga da bata gari na amfani da ita domin kai hare-hare, fashi, ko sufurin makamai a Najeria.

Ga mutane da yawa wadanda basu da halin mallakar mota, babur shine abu mafi sauki da suke amfani dashi domin sufurin iyalansu, da sauran harkokin rayuwa.

Wannan sanarwa dai ta zo ne kwana uku bayan da aka kaiwa sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero farmaki, a lokacin da yake kan hanyarshi ta zuwa gida daga saukar Qur'ani a cikin birnin Kano. A wannan hari, mutane shida ne suka rasa rayukansu, wasu kuma sun jikkata.

A halin da ake ciki dai, Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso baya gari a lokacin da wakilinmu ya neme shi domin jin karin bayani.
XS
SM
MD
LG