Gungun mutane da suka fusata sun hallara a gaban karamin ofishin jakdancin, suka banka masa wuta.
Ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta tabbatar da harin kuma ta ce gwamnati ta hada karfi da ‘yan kasar Libiya domin su tsare ginin. Wata sanarwa ta ce cikin wani lafazi mafi karfi Amurka ta yi tur da Allah wadai da wannan hari da aka kai kan ofishin jakadancin ta.
Haka kuma an yi tarzomar nuna kin jinin Amurka saboda siliman din a kofar ofishin jakadancin Amurka a Alkahira, babban birnin kasar Masar. Wadanda su ka yi zanga-zangar a kasashen duka biyu sun ce siliman din wanda aka yi a Amurka ya ci mutuncin Annabi Muhammad (SAW).