Kamfanin wallafa litattafai da ake kira “Dutton” yace wani soja na musamman daga cikin wadanda suka kai harin, wadda yake amsa sunan Mark Owen, kodashike ba wannan ne ainihin sunansa ba, tareda hadin guiwa da wani dan jarida Kevin Mauer, ne suka rubuta littafin
.
Mawallafin littafin ya fidda sanarwa ta bakin kamfanin wallafa litattafan, cewa “lokaci yayi na bayyana yadda aka gudanar da harin kan maboyar Osama Bin laden,a wani kauyen Pakistan” mutuminda ya kitsa harinda aka kawo kan Amurka a 2001.
Sai dai kakakin ma’aikatar tsaro ta Pentagon da takwaran aikinsa na CIA, duk suka ce basu sami kofin littafin su duba domin a tabbatar da cewa ba a fallasa sirrin gwanati ba.
Ana bukatar tsoffin sojoji da masu aikin leken asiri, su gabatarwa hukumominsu litattafai da suka rubuta, domin a tantance cewa ba a bayyana sirrin gwamnati ba.
Littafin yana fitowa a dai dai lokacinda wasu suke sukar lamirin gwamnatin Obama cewa, ta fallasa asiran gwamnati kan harinda aka kaiwa Bin Laden, saboda wata manufar siyasa kawai.