Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Tabbatar Da Bullar Kwayar Cutar Murar Tsuntsaye Mai Kisa A Italiya Da Girka Da Bulgariya


Hukumomi sun tabbatar da bullar jinsi mai yin kisa na kwayar cutar murar tsuntsaye, H5N1, a kasashen Italiya da Girka da kuam Bulgariya.

Ministan kiwon lafiya na Italiya, Francesco Storace, ya ce jami'ai sun gano matattun agwagin daji dauke da kwayar cutar a Puglia da Calabria a kudancin Italiya, da kuma a tsibirin Sicily.

Jami'an kasar Girka kuma suka ce gwaje-gwajen da aka gudanar a wani dakin binciken kimiyya na Britaniya sun tabbatar da cewa matattun agwagin daji da aka gano a kusa da birnin Salonika na arewacin kasar sun mutu ne a sanadin cutar murar tsuntsaye.

Jami'an Tarayyar Turai suka ce wannan dakin binciken kimiyya na Britaniya ya kuma tabbatar da kasancewar jinsin H5N1 na kwayar cutar murar tsuntsaye a jikin agwagin dajin a arewacin Bulgariya. Jami'ai a kasar Romaniya makwabciyar Bulgariya sun bayar da rahoton sabbin kamuwa da cutar da ake kyautata zaton murar tsuntsaye ce a yankin makwararin ruwan kogin Danube.

A wasu wuraren kuma, a ranar jumma'a kasashen Sin da Indonesiya sun bayar da rahoton mutuwar mutum guda-guda a kasashensu a sanadin murar tsuntsaye.

Wannan cuta ta kashe mutane kusan casa'in a fadin duniya tun 2003. Kwararru suka ce tsuntsaye masu yin kaura sune suke yada wannan cuta.

Jami'an kiwon lafiya na duniya su na kokarin hana barkewar annobar murar tsuntsaye a fadin duniya.

XS
SM
MD
LG