"Abin da ke faruwa a Gaza ba kisan kare dangi ba ne, mun yi watsi da hakan," in ji Biden a wani taron watan al'adun Yahudawa na Amurka a fadar White House.
A cikin kwanaki masu zuwa, ana sa ran sojojin Amurka da ke gabashin tekun Bahar Rum za su hada karshen daya gefen harabar wata dirkekiyar tashar jirgin ruwa - mai tsawon filayen wasan kwallon kafa na Amurka guda biyar a gabar teku a arewacin Gaza.
Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Kurt Campbell ya fada a ranar Litinin cewa gwamnatin Biden ba ta ganin akwai yuwuwar Isra’ila ta samu “cikakkiyar nasara” wajen fatattakar Hamas a yankin Gaza na Falasdinu.
Shugaba Joe Biden ya fada jiya Laraba cewa ba zai aika da muggan makamai ga Isra'ila da za ta iya amfani da su wajen kai hare-haren wuce gona da iri kan Rafah ba, wanda yake tungar karshe ta Hamas a Gaza, saboda nuna damuwa kan yadda zai afka kan fararen hula fiye da miliyan 1 da ke fakewa a wurin.
A ci gaba da shari'ar tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, wadda ake yi a New York, tauraruwar fina finan batsa, Stormy Daniels, ta yi bayani mai cike da batsa jiya a kotun.
Duk da cijewar da tattaunawar Isira'ila da Hamas ta yi, Amurka na fatan bangarorin biyu za su cimma jituwa kan sauran bambancin da ke tsakaninsu don a samu tsagaita wuta.
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birnin Dallas na kasar Amurka, domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron kasuwanci na Amurka da Afirka na 2024 wanda kungiyar kamfanoni kan Afirka ta shirya.
Mutanen 19 da suka fito daga rukuni daban-daban da shugaban Amurka Joe Biden ya karrama a ranar Juma'a saboda yin abin da Fadar White House ta kira a tsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen bada gudunmawa a bangarori daban-daban, da tsaron Amurka da wasu muhimman ayyuka ga al'umma.
Amurka za ta bayar da kusan dala miliyan 55 don magance matsalar jin-kai a Burkina Faso, in ji jami’ar bayar da agaji ta Amurka Samantha Power a ranar Alhamis, a cewar wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya gani.
A ranar Talata ne aka yanke wa Changpeng Zhao, tsohon shugaban kamfanin Binance, hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni hudu, bayan da ya amsa laifinsa na keta dokokin Amurka kan safarar kudade a babbar kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.
Sojojin kasar Mali sun kashe Abu Huzeifa, kwamandan kungiyar Da'ish a yammacin Afirka, a wani gagarumin farmaki da suka kai a yankin Menaka da ke arewacin kasar, a cewar sanarwar da hukumomin Malin suka karanta a gidan talabijin din kasar a ranar Litinin din nan.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatocin Burtaniya da Amurka suka fitar ta yi Allah wa dai da kashe-kashen fararen hula da aka yi a kasar Burkina Faso.
Domin Kari
No media source currently available
Amurkawa da dama da za su yi zabe a watan Nuwamba, batutuwan da suka shafi Afirka ba su dame su sosai ba. Sai dai masu sharhi na ganin duk wanda ya yi nasara a zaben, yana da jan aiki na dawowa kimar Amurka a nahiyar ta Afirka.
Har yanzu matsalar cin hanci da rashawa ta na da girma sosai a kasashen nahiyar, ciki har da Ghana. A cewar hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar, kashi 20 cikin dari na kasafin kudin kasar ya na silalewa ne saboda matsalar cin hanci da rashawa.
A kowacce shekara, dubban ‘yan Najeriya su na kai rahoton almundahana ga hukumomi. A 2021, kimanin korafe-korafe dubu 140 ne a ka shigar, wanda shi ne lamari mafi yawa a cikin shekaru hudu, a cewar hukumar ta EFCC.
Amurkawa za su yi zabe a watan Nuwamba, batutuwan da suka shafi Afirka ba su dame su sosai ba. Sai dai masu sharhi na ganin duk wanda ya yi nasara a zaben, yana da jan aiki na dawowa kimar Amurka a nahiyar ta Afirka.
Wani matashi a garin Larabar Abasawa dake karamar hukumar Gezawa ya cinnawa wani masallaci wuta yayin da mutane suke sallar asubahi. Rundunar ‘yan sadan jihar ta ce mutumin ya zuba fetur ne, ya banka wuta, sannan ya rufe kofar masallacin. Kimanin mutane 35 ne suka samu raunukan sakamakon al'amarin.
Bayan kawancen soji dake tsakanin kasashen biyu, a yanzu haka kasar ta Rasha ta bullo da wani sabon tsari na koyar da harshen kasarta a makaratun Nijar. Yayin da wasu ‘yan Nijar ke alfahari da shirin, wasu kuwa jan hankalin hukumomin kasar suke yi a game da matsalar da za a iya samu.