Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaftarewar Kasa A Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Ta Kashe Akalla Mutane 12


Zaftarewar Kasa
Zaftarewar Kasa

Zaftarewar kasar ta afku ne da tsakar ranar Asabar a gundumar Dibaya Lubwe da ke lardin Kwilu.

Akalla mutane 12 ne suka mutu yayin da wasu fiye da 50 suka bace bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya yi sanadin ruftawar wani rafi a kudu maso yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, in ji wani jami'in yankin da kuma wani shugaban kungiyoyin fararen hula a ranar Lahadi.

Zaftarewar kasar ta afku ne da tsakar ranar Asabar a gundumar Dibaya Lubwe da ke lardin Kwilu.

Zaftarewar kasa
Zaftarewar kasa

Gwamnan lardin na rikon kwarya Felicien Kiway ya ce kawo yanzu an zakulo gawarwaki 12 daga cikin baraguzan da suka hada da mata tara da maza uku da kuma jariri daya.

“Kusan mutane 50 ne suka bace amma muna ci gaba da binciken cikin laka,” in ji shi, inda ya kara da cewa yiwuwar sake gano wadanda suka tsira da ransu zai yi wuya domin lamarin ya faru ne sa’o’i 12 kafin binciken.

Kodinetan wata kungiyar farar hula ta yankin, Arsene Kasiama, ya ce zaftarewar kasar ta kuma fada kan mutanen da ke sayayya a wata kasuwa.

Ya bayar da adadin mutuwar mutane 11, tare da wasu mutane bakwai da suka samu munanan raunuka, yayin da sama da mutane 60 suka bace.

Rashin tsarin birane da tsufar ababen more rayuwa a fadin Kongo ne ya sa al'ummomi ke fuskantar matsaloli sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda ke kara zafafa da yawa a Afirka saboda dumamar yanayi, a cewar masana yanayi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG