Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 54 Sun Mutu Sakamakon Zaftarewar Kasa A Kudancin Philippines


Zaftarewar Kasa A Kudancin Philippines
Zaftarewar Kasa A Kudancin Philippines

Adadin wadanda suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a wani kauye inda ake hakar zinari a kudancin kasar a cewar hukumomin kasar.

Zaftarewar kasar ta afku ne a kauyen Masara dake kan tsauni a lardin Davao de Oro a daren ranar Talata bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe makonni ana yi.

Gwamnatin lardin Davao de Oro ta fada a wani sako da ta wallafa a Facebook cewa an gano gawarwaki 54. Aƙalla mazauna kauyen 32 sun tsira da raunuka amma wasu 63 sun ɓace, in ji shi. Daga cikin wadanda suka bace har da masu hakar zinari da ke cikin motocin bas biyu suna jira a kai su gida a lokacin da zaftarewar kasar ta rutsa da su ta kuma binne su.

Aikin nema da ceto ya fuskanci cikas sakamakon rashin kyawun yanayi da kuma fargabar sake aukuwar zabtarewar kasa. Sama da iyalai 1,100 aka kwashe zuwa cibiyoyin tsugunnar da mutane don kare su, in ji jami’an bayar da agajin gaggawa.

Yankin dai ya yi ta fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya tsawon makonni kafin zaftarewar kasar ta afku. Haka kuma girgizar kasar ta lalata gidaje da gine-gine a yankin a cikin 'yan watannin nan, in ji jami'ai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG