Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani ‘Dan Najeriya Na Kokarin Kafa Tarihi A Wasan Chess Don Neman Ilmantar Da Yara Miliyan 1 A Afirka


‘Dan Najeriya Mai Gasar Wasan Chess Na Tsawon Lokaci Na Duniya A Birnin New York
‘Dan Najeriya Mai Gasar Wasan Chess Na Tsawon Lokaci Na Duniya A Birnin New York

Wani zakaran dara na wasan Chess, ‘dan Najeriya kuma mai fafutukar koyar da ilimin yara yana kokarin buga dara na tsawon sa'o'i 58 ba tare da tsayawa ba a dandalin Times Square na birnin New York domin karya tarihin duniya na tsawon wasan chess mafi dadewa.

WASHINGTON, D. C. - Tunde Onakoya, mai shekaru 29, yana fatan tara kudi dala miliyan 1 don ilimantar da yara a fadin Afirka. Yana fafata wasan ne da Shawn Martinez, zakaran chess na Amurka, daidai da ka'idodin Guinness World Record cewa wajibi ne 'yan wasan biyu su yi duk wani ƙoƙari na zarta tarihin da aka kafa, inda za su ci gaba da fafata wasan har na tsawon lokacin.

‘Dan Najeriya mai wasan gasar Chess
‘Dan Najeriya mai wasan gasar Chess

Onakoya ya buga wasan daran har na tsawon sa'o'i 42 da karfe 10:00 na safe agogon GMT a ranar Juma'a. Goyon baya na karuwa ta yanar gizo da kuma wurin wasan, inda ake jin wakokin Afirka da masu kallo suka sa da magoya baya, suna kuma murna da tafin karfafa 'yan wasan.

Tarihin mafi tsawon wasan dara na Chess a yanzu shine sa'o'i 56, mintuna 9 da dakika 37, wanda Hallvard Haug Flatebø da Sjur Ferkingstad suka kafa a shekarar 2018, dukkansu daga kasar Norway.

‘Dan Najeriya mazaunin New York mai wasan gasar Chess
‘Dan Najeriya mazaunin New York mai wasan gasar Chess

Yunkurin sa na kafa tarihin na da manufar "samarwa miliyoyin yara a fadin Afirka ilmi wadanda ilimi ba ya kai wa garesu," in ji Onakoya, wanda ya kafa kungiyar wasan Chess in Slums Africa a cikin 2018. Kungiyar na son tallafa wa don ilmantar da akalla yara miliyan 1 marasa galihu a fadin nahiyar.

"Ina da kwarin gwiwa dari bisa dari a yanzu saboda mutanena suna nan suna bani goyon baya da kiɗa," in ji Onakoya da yammacin Alhamis bayan 'yan wasan sun haye sa'o'i 24 suna gwabzawa.

A batun abinci na Onakoya, ya na shan ruwa da yawa da shinkafa dafa-duka, ɗaya daga cikin sanannun abincin Yammacin Afirka.

Lokacin da yake koyarwa yara wasan Chess
Lokacin da yake koyarwa yara wasan Chess

Ga kowace sa'a ta wasan da aka buga, Onakoya da abokin karawarsa suna samun hutun mintuna biyar kacal. Wani lokaci ana haɗa hutun wuri ɗaya, kuma Onakoya yana amfani da su don tattaunawa da 'yan Najeriya da na New York da ke wurin suna karfafa masa.

An tara dalar Amurka 22,000 a cikin sa'o'i 20 na farko na yunkurin, in ji Taiwo Adeyemi, manajan Onakoya.

"Samun goyon bayan ya kasance mai yawa daga 'yan Najeriya a Amurka, shugabannin duniya, shahararrun mutane da daruruwan masu wucewa," in ji shi.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG