Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine Ta Yi Jana'izar Mutanen Da Suka Mutu Sakamakon Kazamin Harin Rasha


APTOPIX Russia Ukraine War
APTOPIX Russia Ukraine War

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce mutane 55 ne suka mutu yayin da wasu 328 suka jikkata a a wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai a Poltava, kan wata cibiyar horar da sojoji da kuma wani asibiti da ke kusa.

A jiya Assabar Ukraine ta yi jana'izar wadanda suka mutu sakamakon hari mafi muni da Rasha ta kai, a yayin da shugabannin hukumomin leken asirin Amurka da na Birtaniya suka ce ci gaba da goyon bayan Ukraine a rikicin da take yi da Rasha na da muhimmanci.

Daruruwan 'yan kasar Ukraine da suka hada da 'yan uwa da ke makoki, sun tattaru a babbar majami’ar Assumption da ke Poltava, domin nuna alhini kan mutane fiye da 50 da suka mutu, yayin da wasu fiye da 300 suka jikkata, a wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan wata cibiyar horar da sojoji da kuma wani asibiti da ke kusa.

Da yammacin ranar Juma'a, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce mutane 55 ne suka mutu yayin da wasu 328 suka jikkata a harin na ranar Talata a Poltava.

Zelenskyy, wanda ke cike da takaicin jan kafa da kawayen kasashen yammacin duniya suke yi kan cire tsauraran sharudan amfani da makaman da suke samarwa, ya ce Ukraine na kera na ta jiragen yaki da makamai masu linzami.

Ya ce "nan ba da jimawa ba Shugaban Rasha Vladimir Putin zai fuskanci matsin lambar neman abu ɗaya kawai: shi ne zaman lafiya."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG