Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Tsohon Dan Majalisar Wakilan Najeriya Mohammed Idris Ya Rasu

Sallar Idi
Sallar Idi

Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Idris ya fadi kuma ya rasu jim kadan bayan kammala Sallar Idi a gidansa da ke Abuja ranar Laraba. Duk da kokarin farfado da shi, Allah ya yi masa rasuwa.

Mohammed Idris, fitaccen jigo a siyasar Najeriya, kuma tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ankpa, Olamaboro, da Omala na tarayya ya rasu.

Rasuwar Mohammed, wanda kuma da ne ga tsohon gwamnan jihar Kogi, Ibrahim Idris, ta bar gibi a fagen siyasa musamman a jiharsa ta Kogi.

Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Idris ya fadi kuma ya rasu jim kadan bayan kammala Sallar Idi a gidansa da ke Abuja ranar Laraba. Duk da kokarin farfado da shi, Allah ya yi masa rasuwa.

Wasu masallata suna sallah a Masallaci
Wasu masallata suna sallah a Masallaci

A bisa al’adar Musulunci, an yi jana’izar Mohammed Idris a makabartar Gudu da ke Abuja bayan sallar jana’izar tare da halartar dimbin jama’a a babban masallacin kasa, tare da 'yan uwa, abokai, abokan aiki, da sauran jama’a.

~Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG