Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Tsohon Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu


Lokacin da ake saka gawar Akeredolu a makwancinta (Hoto: Facebook/Oyo News)
Lokacin da ake saka gawar Akeredolu a makwancinta (Hoto: Facebook/Oyo News)

Akeredolu ya rasu a kasar Jamus a ranar 27 ga watan Disambar bara bayan fama da rashin lafiya. Shekarunsa 67.

An gudanar da jana’izar tsohon Gwamnan jihar Ondo marigayi Rotimi Akeredolu a mahaifarsa ta Owo da ke jihar wacce kudu mas yammacin Najeriya.

A ranar 27 ga watan Disambar bara Akeredolu ya rasu a Jamus inda ya je neman magani saboda fama da rashin lafiya. Shekarunsa 67.

An fara jana’izar ce da taron addu’o’i a Mujami’ar St. Andrews kafin daga bisani a binne shi.

Manyan jami’an gwamnatin jihohi da na tarayya da suka halarci taron janai’zar sun hada mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettimah.

Kazalika Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan Oyo Seyi Makinde da shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje duk sun halarci taron jana'izar.

Yayin jawabinsa, Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ya gaji Akeredolu, ya kwatanta marigayin a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa don kare jama’a.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG