Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban TikTok Yana Tsammanin Samun Nasara A Tsarin Dokar Amurka: 'Ba za mu je ko'ina ba'


USA-TIKTOK
USA-TIKTOK

Babban jami’in gudanarwa na TikTok ya fada a ranar Laraba cewa kamfanin sadarwar na sa ran samun nasara a kalubalantar dokar toshe manhajar da Shugaba Joe Biden ya sanya wa hannu wadda ya ce za ta hana yada gajerun bidiyon da Amurkawa miliyan 170 ke

WASHINGTON, D. C. - "A tabbata ba za mu je ko'ina ba," in ji Shugaban kamfanin Shou Zi Chew a cikin wani faifan bidiyo da aka buga 'yan mintuna kadan bayan Biden ya rattaba hannu kan kudirin dokar da ta baiwa ByteDance na kasar Sin kwanaki 270 don karkatar da kadarorin Amurka na TikTok ko kuma a dakatar da shi. "Gaskiya da Kundin Tsarin Mulki suna nan a gefenmu kuma muna sa ran sake yin nasara."

Sa hannun Biden ya tsaida ranar 19 ga Janairu a karshe ranar siyarwa, kwana guda kafin wa'adinsa ya ƙare, amma zai iya tsawaita wa'adin da watanni uku idan ya yanke shawarar ByteDance yana samun ci gaba. Biden na neman wa'adi na biyu inda ya ke karawa da tsohon shugaban kasar Donald Trump.

Kakakin fadar White House Karine Jean-Pierre ta fada a ranar Talata cewa "Ba ma son ganin an hana." Ta kara da cewa, "Wannan game da mallakar PRC ne," yayin da take magana kan Jamhuriyar Jama'ar Sin.

A shekarar 2020, kotuna sun hana Trump dakatar TikTok da WeChat mallakar 'yan China, rukunin Tencent 0700.HK a Amurka.

Trump, ‘dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, ya sauya furcin sa kuma ya ce a ranar Litinin Biden yana "ingiza" dakatar da TikTok kuma shi ne ke da alhakin idan aka sanya dokar, yana mai kira ga masu jefa kuri'a da su lura.

"Babu ko tantama wannan doka ce a kan TikTok," in ji Chew, yana mai jaddada cewa TikTok zai ci gaba da aiki yayin da kamfanin ke kalubalantar hana ayyuka.

Masana da yawa suna tambaya ko akwai wani mai siye wanda ke da albarkatun kuɗi don siyan TikTok kuma idan China da hukumomin gwamnatin Amurka za su amince da siyarwa.

Sakamakon damuwar da ‘yan majalisar dokokin Amurka ke da shi na cewa China za ta iya kutse cikin bayanan Amurkawa ko kuma ta sanya ido a kan manhajar, a ranar Talata ne majalisar dattawan ta Amurka ta zartar da kudirin dokar. Majalisar wakilan Amurka ta amince da shi a ranar Asabar.

An shirya cewa TikTok za ta ƙalubalanci kudirin na farko kuma ana sa ran masu amfani da TikTok za su sake ɗaukar matakin doka. Wani alkali na Amurka a Montana a watan Nuwamba ya toshe dokar hana TikTok a jihar, saboda dalilai na izinin fadin yawun bakin ‘dan adam.

Kungiyar Kare 'Yancin Bil'adama ta Amurka The American Civil Liberties Union ta ce haramtawa ko neman karkatar da TikTok zai "saka wani abin ban tsoro a duniya game da wuce gona da iri na sa hannu gwamnati kan dandamalin kafofin watsa labarun."

Amma, sabuwar dokar tana iya bai wa gwamnatin Biden kafaffen doka mai ƙarfi don hana TikTok idan ByteDance ta gaza karkatar da manhajar, in ji masana.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG