Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Biden Ya Gabatar Da Shirin Ba Wadanda Su Ka Auri Amurkawa Izinin Zama Kasar


Biden Immigration
Biden Immigration

Shugaba Joe Biden ya sanar da wani sabon tsari da zai ba wadanda su ka auri Amurkawa, da kuma 'ya'yan mutanen da su ka auri Amurkawa, izinin zama kasar din-din-din.

Matakin ya shafi kusan ma'aurata rabin miliyan Amurkawa da yara 50,000 wadanda ba 'yan asalin kasar ba wadanda iyayensu su ka auri Ba’amurke.

Da yake sanar da shirin, Shugaba Biden ya ce,"Sun shafe a kalla shekaru goma suna zaune a nan Amurka. Wadannan ma'auratan suna renon iyalai, suna tura 'ya'yansu Coci da makaranta, suna biyan haraji, suna ba da gudummawa ga kasarmu na tsawon shekaru goma ko fiye. A gaskiya ma, tsawon shekarun da mutanen da abin ya shafa suka shafe a nan shine shekaru 23, amma suna zaune a Amurka duk wannan lokacin, cikin tsoro da rashin tabbas za mu iya gyara wannan yau, kuma abinda mu ke yi ke nan."

Shugabar kungiyar 'yan Majalisar Dokokin Amurka Spaniyawa tana magana bayan sanarwar Biden
Shugabar kungiyar 'yan Majalisar Dokokin Amurka Spaniyawa tana magana bayan sanarwar Biden

Kafin dan gudun hijira ya iya cin moriyar sabon tsarin, tilas ne ya zauna a Amurka na tsawon shekaru 10 ko fiye, kuma ya kasance yana auren Ba’amurke bisa dokar kasa, a ranar 17 ga watan Yuni, 2024, bisa ga cewar wata takardar bayanai ta fadar White House.

Har ila yau, a cikin sanarwar ta Shugaba Biden, akwai shirin samar da bizar aiki ga wadanda su ke cikin rukunin yaran da iyayensu bakin haure, su ka shiga kasar su ka sa su makaranta da ake kira DACA, wadanda ke da takardar shaidar samun digiri na Amurka da kuma tayin aikin yi da ya shafi kwarewar su.

Joe Biden lokacin da ya sanar da sabon tsare kare ;yan cirani
Joe Biden lokacin da ya sanar da sabon tsare kare ;yan cirani

Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wata guda da Shugaba Biden ya dauki matakin zartaswa kan shige da fice - kuma a bisa doka. A farkon watan Yuni, ya yi amfani da ikon shugaban kasa da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya sha amfani da shi wajen hana mafaka ga galibin bakin haure da ke bi ta kan iyakar Amurka da Mexico su ka shiga Amurka.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG