Kasar Iran mai rinjayen mabiya Shii’a da Saudi Arabiya mai rinjayen mabiya Sunni, sun amince da maido da huldar diplomasiyya a tsakanin su, da sake bude ofisoshin jakadancin su a kasashen juna ne, biyo bayan cimma yarjejeniyar da China ta samar aka sanar a watan Maris.
Dangantaka tsakanin Riyadh da Tehran ta ruguje ne a shekarar 2016, bayan da aka kai hari kan ofishin jakadancin Saudiyya dake Iran, yayin wata zanga zangar nuna fushi kan kisan da Riyadh din ta yima babban malamin Shii’ar nan Nimr al-Nimr.
"Shugabannin Saudiyya sun fahimcin muhimmancin karfafa dangantaka, kara fadi tashi, da fadada dangantaka,’’ Abinda jakadan Saudiyyar a Iran Abdullah Alanazi ya fada kenan, a yayin da ya isa birnin Tehran domin fara aiki, cewar sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya.
Haka shima, a ranar ta Talata, jakadan Iran a Saudi Arabiya, Alireza Enayati, ya isa babban birnin kasar Riyadh, inda jami’an ma’aikatar harkokin waje da ma’aikatan ofishin jakadancin suka karbe shi, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin Iran, IRNA ta sanar.
A can baya Alanazi shine jakadan Saudi Arabiya a Oman, yayin da Enayati ya kasance, wakilin Iran a kasar Kuwait.
A watan jiya ne, ofishin jakadancin Saudiyya ya maido da fara aiki a Tehran. Ita kuwa Iran ta sake bude ofishin jakadancin ta a Riyadh ne, a watan Yuni, tare da daga tuta a yayin wani buki.
A watan jiya, babban jami’in diplomasiyyar Iran, Ministan harkokin wajen ta Hossein Amirabdollahian, yayi hudubar samar da hadin kai da tattaunawa, a yayin ziyarar sa ta farko a kasar Saudi Arabiya tun bayan bayyana sake dinkewar kasashen, inda yace, huldar da ta dawo tsakanin kasashen na tafiya bisa turba.
Kashen Iran da Saudi Arabiya dai sun rika mara baya ga bangarori dabam dabam a yankunan dake fama da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya na tsawon shekaru.
~ Hauwa Sheriff
Dandalin Mu Tattauna