Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar Na Kokarin Sasanta Isra'ila da Hamas Don Kauracewa Barkewar Yaki - Majiyar Masar


Shugaban kasar Masar - Abdel Fattah El-Sisi
Shugaban kasar Masar - Abdel Fattah El-Sisi

Majiyoyin tsaron Masa biyu sun sanar a ranar Litinin cewa Masar tattaunawa da Isra'ila da Hamas don kokarin hana barkewar yaki a tsakaninsu da kuma tabbatar da tsaron Isra'ilawa da mayakan Falasdinawa suka yi garkuwa da su.

Masar ta bukaci Isra’ila da ta yi taka-tsan-tsan, sannan Hamas da ta rike mutanen da ta kama cikin yanayi mai kyau domin a bude yiyuwar sulhu nan ba da jimawa ba, duk da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a jere a zirin Gaza ya sanya sasantawa ta yi wuya, in ji majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu.

Mayakan Falasdinawa sun yi garkuwa da mutane da dama a wani harin da kungiyar Hamas ta kaddamar daga zirin Gaza a ranar Asabar, wanda ya hada da sojoji da fararen hula, yara da kuma tsofaffi. Wata kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu mai suna Islamic Jihad ta ce tana rike da sama da 30 na wadanda aka kama.

Jiragen yakin Isra'ila da jirage masu saukar ungulu da makaman atilare sun yi ta luguden wuta a zirin Gaza a daidai lokacin da Isra'ila ke fafatawa don fatattakar mayakan Falasdinawa da suka tsallaka daga Gaza.

Yankin Sina'i na Masar yana da iyaka da zirin Gaza da kuma Isra'ila, kuma Masar ta kasance mai shiga tsakani ta Isra'ila da kungiyoyin Falasdinawa a rikicin da ya faru a baya.

Majiyoyin tsaron Masar sun ce wasu 'yan yawon bude ido 7,000 sun dawo daga Sinai zuwa Isra'ila tun bayan barkewar fadan. Kungiyar agaji ta Red Crescent ta kuma kai agajin jinya zuwa Gaza daga Sinai ta mashigar Rafah.

A ranar Lahadin da ta gabata, an harbe wasu 'yan yawon bude ido biyu 'yan Isra'ila da wani jagora dan kasar Masar a wani wurin binciken kayan tarihi da ke birnin Alexandria da ke arewacin Masar.

Majiyar tsaron ta ce an mika dan sandan Masar din da ake zargi da aikata kisan zuwa kotun soji.

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na EgyptAir tsakanin Cairo da Tel Aviv har sai yadda hali yayi, yayin da jirage daga Sharm el-Shiekh na kudancin Sinai zuwa Tel Aviv ke ci gaba da aiki a yau Litinin, abin da ya baiwa Isra'ilawa masu yawon bude ido damar komawa gida, in ji majiyoyin tashar jirgin saman Masar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG