Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Da Isra’ila Ta Kai Ta Sama Ya Kashe Mutane 14 A Gaza - Hamas


Rikicin Isira'ila Da Falasdinawa
Rikicin Isira'ila Da Falasdinawa

Ma’aikatar Lafiyar ta ce harin na Isra’ila, ya auku ne a Khan Younis, wanda ke kudancin Gaza, kuma cikin wadanda su ka mutu din har da yara tara.   

Wani harin jirgin sama da Isra’ila ta kai Gaza yau Alhamis, ya hallaka mutane 14, a cewar Ma’aikatar Lafiyar Gaza, wadda kungiyar Hamas ke tafi da ita, yayin da Isra’ila ta kaddamar da wasu sabbin hare haren jiragen sama, da jerin farmaki daga ta kasa, kan kungiyar mayakan ta Falasdinu.

Ma’aikatar Lafiyar ta ce harin na Isra’ila, ya auku ne a Khan Younis, wanda ke kudancin Gaza, kuma cikin wadanda su ka mutu din har da yara tara.

Isra’ila ba ta ce komai a kan harin ba kai tsaye, to amma ta bayar da rahoton kai hari a Khan Younis, wanda ta ce ya hallaka wasu ‘yan bindiga uku, wadanda su ka yi yinkurin dasa bam.

Rundunar sojin Isira’ila ta ce sojojinta na kasa sun kashe biyu daga cikin mayakan a wani gini da ke kusa da wurin.

Har ila yau Isira’ila ta ba da rahoton cewa a ranar Alhamis ta sake kai wasu sabbin hare-hare kan wuraren da kungiyar Hezbullah ta ke a kudancin kasar Labanon da kuma harba makamin roka daga Labanon zuwa Isira’ila.

Hare haren na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah, a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin, ya gargadi Isra’ila kan kai hari Labanon.

Nasrallah ya ce “idan makiya suna tunanin kaddamar da yaki a kan kasar Labanon, za mu yi yaki ba tare da kakkautawa ba, ba tare da ka’ida ba, ba tare da iyaka ba, kuma ba tare da takura ba.”

Kalaman nasa sun biyo bayan wani hari da jirgi mara matuki ya kai da ya kashe wani babban jami’in Hamas a Beirut, babban birnin kasan Labanon.

Hamas da jami’an tsaro a yankin sun danganta harin da ya kashe Saleh al-Arouri da harin da wani jirgi mara matuki na Isra’ila ya kai, ko da yake Isra’ila ba ta dauki alhakin kai harin kai tsaye ba.

Shugaban Hukumar Leken Asirin Isra’ila, Mossad, David Barnea, a ranar Laraba, ya ce hukumar za ta farauto duk wani dan Hamas da ke da hannu a harin da aka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, ko a ina suke.

Hezbullah, kamar Hamas, kungiyar gwagwarmayar da Iran ke marawa baya, wacce Amurka ta ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci, tana harba makaman roka a kan iyakar arewacin Isra’ila, tun bayan barkewar yakin Isra’ila da Hamas a watan Oktoban bara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG