Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Jirgin Kasa A Chile Ya Kashe Mutane 2 Da Jikkata Wasu Da Dama


Hadarin jiragen kasa biyu a Santiago, Chile safiyar Alhamis Yuni 20, 2024
Hadarin jiragen kasa biyu a Santiago, Chile safiyar Alhamis Yuni 20, 2024

Akalla mutane biyu ne suka mutu yayin da wasu tara suka jikkata yau Alhamis a lokacin da wani jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi ci karo da wani jirgin kasa mai gwajin aiki a babban birnin kasar Chile, Santiago.

Ana dai ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin, wanda ya kifar da wani karagon jirgin gaba daya a saman wani karagon daya jirgin.

Santiago, Chile
Santiago, Chile

Jirgin, wanda ke dauke da tan 1,346 na tagulla, yana kuma cike makil ne da mutane, yayin da daya jirgin na da ma'aikata 10 a ciki da ke aikin gwajin saurin gudun jirgin, in ji kamfanin jirgin kasa.

Santiago, Chile
Santiago, Chile

Hukumomi ba su tantance mutanen biyu da aka kashe ba. Mutanen tara da suka jikkata sun hada da ‘yan kasar China hudu da ke karbar magani a asibitocin da ke kusa da wurin da hatsarin ya afku a San Bernardo na kasar Chile.

Santiago, Chile
Santiago, Chile

Ministan sufuri Juan Carlos Muñoz ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa "Dole ne mu gano mene ne musabbabin hadarin kuma mu dauki matakan da suka dace."

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG