Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Da Trump Zasu Fafata Muhawara Karon Farko A Yau Alhamis 


Zaben Shugaban Kasa Ta Farko
Zaben Shugaban Kasa Ta Farko

Donald Trump da Joe Biden zasu yi muhawararsu ta farko akan yakin neman zabensu, inda kowannensu ke fada wa masu kada kuri'a cewa, zaben dayan zai zama babban kuskure

Masana sun ce wannan muhawara da za a yi ta bambanta da sauran na baya, inda zata hada shugaba mai ci da kuma tsohon shugaban kasa.

A bayaninsa yayin yakin neman zabe, Trump yace Biden yana lalata kasar. Yana mai cewa,

"Farashin kayayyaki sai hauhawa su ke. Ana samun masu aikata manyan laifuka na wuce gona da iri. Kasashen Turai na cikin rudani, Gabas ta Tsakiya na fama da rikice-rikice, Iran na kara samun karfin gwiwa. China ta dauko hanya. Sannan wannan shugaban na jan mu zuwa ga yakin duniya na uku.”

Donald Trump
Donald Trump

A nashi bayanin, Biden ya ce Trump zai mayar da kasar baya.

"Duk wani ci gaba, duk wani 'yanci, da dama da ake da su na tattare da hadari. Trump yana kokarin ganin kasar ta manta da yadda abubuwa suka kasance cikin duhu da rashin tabbas a lokacin da yake shugaban kasa. Ba za mu taba mantawa ba,"

Joe Biden
Joe Biden

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa ‘yan takarar na tafiya keke-da-keke, abin da ke kara jan hankalin jama'a a muhawarar da za a yi, a cewar farfesa a fannin aikin jarida na jami'ar Northeastern Alan Schroeder.

"Ina ganin hakan zai kara nawaita wa 'yan takarar biyu, ta fuskar damar da muhawarar zata ba su, da kuma hadarin da ke tattare da muhawarar," a cewar Schroeder.

Wannan muhawara da za a yi ta bambanta da sauran na baya, inda zata hada shugaba mai ci da kuma tsohon shugaban kasa, a cewar farfesa a fannin sadarwa ta Jami'ar Pennsylvania Kathleen Hall Jamieson.

Kathleen ta ce, “To, “jama’a na da masaniya akan dukkan wadannan ‘yan takarar a matsayinsu na mutane, ta yiwu su fi sanin halayensu, da dabi’unsu. Amma a bana, saboda shekarun ‘yan takarar biyu, akwai bukatar, ko da kana tunanin ka san abubuwa da yawa akan dukkansu, wanda ba mamaki a bana ka sani, zaka iya cewa, shin tunaninsu da hankalinsu sun cancanta da zama shugaban Amurka?"

Muhawarar siyasa ta kunshi bayyana sako da ra’ayi, a cewar masanin harkokin siyasa Brett O’Donnell.

Biden da Trump
Biden da Trump

"Dole ne ku tura sako akai-akai a lokacin muhawarar, amma kuma kana so ka yi amfani da wannan damar ka bayyana wani muhimmin abu, wanda 'yan jarida za su maida hankali akansa, wanda kuma zai baka damar yin tasiri a muhawarar," a cewar O’Donnell.

Wannan ce zata zama muhawarar shugaban kasa ta farko a tarihin Amurka, in da ba a tsaida Trump ko Biden a matsayin ‘yan takarar jam’iyyarsu ba a hukumace. Ba za a yi wani jawabin bude zaman muhawarar ba a daren Alhamis. Sannan za a kashe na’urar daukar magana ta 'yan takarar biyu idan ba lokacin yin bayaninsu bane.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG