Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazanar Amurka Kan Hana Mu Makamai Ba Za Ta Sa Mu Dena Kai Hari Gaza Ba - Netanyahu


Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu Mayu 5, 2024. (Photo by Menahem Kahana/AFP)
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu Mayu 5, 2024. (Photo by Menahem Kahana/AFP)

Firaiminista Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Alhamis cewa barazanar da Amurka ta yi na hana makamai ba za ta hana Isra’ila ci gaba da kai hare-hare Gaza ba, lamarin da ke nuni da cewa za ta iya yin gaban kanta wajen mamaye birnin Rafah mai cunkoson jama’a ba tare da goyon bayan babbar kawarta ba

WASHINGTON, D. C. - Shugaba Joe Biden ya bukaci Isra'ila da kada ta ci gaba da gudanar da irin wannan harin saboda fargabar za ta kara tsananta bala'in jin kai a yankin Falasdinu.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

A ranar Larabar da ta gabata ne, ya ce Amurka ba za ta baiwa Isra’ila makaman da za ta kai farmakin Rafah ba, lamarin da ke kara matsin lamba kan Netanyahu.

Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Netanyahu ya ce "idan ya zamana dole ne mu tsaya mu kadai, za mu tsaya mu kadai. Idan har ta kama, za mu yi fada da faratanmu. Amma muna da fiye da farata.”

Babban mai magana da yawun sojin Isra’ila, Rear Adm. Daniel Hagari, shi ma ya bayyana yin watsi da tasirin duk wani hanasu makamai. "Sojoji suna da alburusai don ayyukan da suke shirin yi, da kuma shirin shiga Rafah, mu ma muna da makaman da muke bukata," in ji shi yayin da yake amsa tambaya a wani taron manema labarai.

Palestinians
Palestinians

Isra'ila ta sha yin barazanar mamaye Rafah, inda Falasdinawa kusan miliyan 1.3, fiye da rabin al'ummar suka nemi mafaka.

Birnin na Rafah, wanda ke kudancin Gaza ya kasance tungar ayyukan jin-kai, wanda ya fuskanci cikas sosai sakamakon rufe manyan mashigar Gaza guda biyu a wannan makon.

Isra'ila ta ce Rafah ita ce tungar karshe ta Hamas kuma dole ne sojojin su shiga idan har suna fatan wargaza kungiyar ta Hamas tare da kwato dumbin mutanen da aka kama a harin na ranar 7 ga watan Oktoba da ya haddasa yakin.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG