Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yi Gaggawar Gudanar Da Bincike Kan Zargin Da Ningi Ya Yi – Atiku


Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)

Atiku ya yi kiran ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce yin rufa-rufa kan lamarin da kuma dakatar da wanda ya kwarmata zancen ba mafita ba ce.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce akwai bukatar a gudanar da kwakkwaran bincike kan zargin cushe a kasafin kudin Najeriya na 2024.

Atiku ya yi kiran ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce yin rufa-rufa kan lamarin da kuma dakatar da wanda ya kwarmata zancen ba mafita ba ne.

A ‘yan kwanakin da suka gabata, Sanata Abdul Ningi da ke wakiltar mazabar tsakiyar yankin jihar Bauchi a Majalisar Dattawa, ya yi zargin cewa an yi cushen sama da Naira tiriliyan uku a kasafin kudin 2024.

Sanata Abdul Ningi
Sanata Abdul Ningi

Majalisar ta musanta zargin ta kuma dakatar da shi tsawon watanni uku daga halartar zaman majalisar bayan da akasarin mambobinta suka amince da hakan.

Sai dai Atiku ya ce ‘yan Najeriya na da hakkin su ga an gudanar da bincike kan zargin da Ningi ya yi.

“Musanta cewa babu wani abu kamar haka, da dakatar da Sanatan da ya kwarmata zancen, ba za su hana zargin cewa akwai matsalar cin hanci da rashawa da kashe kudade ba bisa ka’ida ba da gwamnatin tarayya ke yi.

“Ba zai yi wu a yi rufa-rufa kan zargin yin cushe a kasafin kudi da yawansa ya kai Naira tiriliyan uku ba.” In ji Atiku.

Zauren Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)
Zauren Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)

Atiku ya kara da cewa, “duba da irin wahalar da ake fuskanta a Najeriya, cushe a kasafin kudin kasa na nufin karin yunwa, talauci, rashin tsaro da rashin wutar lantarki da matsalar canja kudaden kasashen waje da kuma tsadar rayuwa.”

“Babu yadda za a ce ‘yan Najeriya za su nade hannayensu suna kallo a yi watsi da wannan zargi da ke kara ta’azzara matsalar tattalin arzikinmu.” In ji Atiku.

Najeriya ta ware Naira tiriliyan 28.7 a matsayin kasafin kudin shekarar 2024.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG