Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Ningi Tsawon Watanni 3 Sakamakon Zarge-Zargen Yin Cushe A Kasafin Kudi


Abdul Ningi
Abdul Ningi

Majalisar Dattawan Najeriya karkashin jagorancin Shugabanta, Godswill Akpabio, ta dakatar da Sanata Abdul Ningi a bisa zarge-zargen yin cushen naira tiriliyan N3.7 a cikin kasafin kudin bana.

WASHINGTON DC - An dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar mazabar Bauchi ta Tsakiya tsawon watanni 3 ne, bayan tafka zazzafar mahawara a zauren majalisar.

Sanata Akpabio, wanda ya bayyana laifin da Ningi ya aikata da "mummuna", ya gudanar da kuri'ar jin ra'ayi ta hanyar murya inda galibin Sanatoci suka goyi bayan dakatar da Sanata Ningi tsawon watanni 3.

A cikin wata hira da aka yi da shi, Sanata Ningi yayi ikrarin cewar gwamnatin tarayya na aiwatar da nau'uka 2 na kasafin kudin bana, kuma kasafin naira tiriliyan 28.7 da gwamnatin tarayya da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanyawa hannu ya maida shiyar arewacin Najeriya saniyar ware.

Sanatoci da dama sun yi ta caccakar Sanata Ningi akan batun, inda suka bayyana zargin nasa da labarin kanzon kurege wanda bai kamata a samu shugaba kamarsa da yada shi ba.

A karshe dai Sanata Ningi ya musanta cewar gwamnatin tarayya na aiwatar da nau'uka 2 na kasafin kudin bana, amma ya dage akan cewar naira tiriliyan 25 na kasafin ne aka warewa ayyuka a yayin da Naira tiriliyan 3.7 basu da nasaba da ayyuka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG