Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Isra'ila Sun Kusa Daina Zafafa Kai Hare-Hare-Netanyahu


Wadansu yara suna wasa a inda mayakan Isra'ila su ka kai hari
Wadansu yara suna wasa a inda mayakan Isra'ila su ka kai hari

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fadi cewa dakarun kasarsa sun kusa kawo karshen "lokacin zafafa kai hare hare kan mayakan Hamas a Gaza na ba da jimawa ba.

Firai Ministan ya kara da cewa, ta yiwu Isra'ila zata tura sojojinta zuwa bakin iyakar kasar da Lebanon, inda dakarun kasar ke fafatawa da ‘yan kungiyar Hezbullah na Lebanon a duk rana.

Fada tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran ya zafafa a 'yan makonnin da suka gabata, abinda ke kara kawo fargabar yiwuwar barkewar rikici a yankin.

Yakin Isra'ila da Falasdino
Yakin Isra'ila da Falasdino

A wata hira da yayi da gidan talabijin din Isra'ila na Channel 14, Netanyahu ya ce tura sojojin zuwa arewacin iyakar kasar zai karfafa tsaron kasar don tunkarar kungiyar Hezbollah, matakin zai kuma ba Isra'ilawan da suka tserewa fadan a kusa da iyakar Lebanon damar komawa gidajensu.

Ya kara da cewa yayin da yake fatan a lalubo hanyar warware rikicin da kungiyar Hezbollah ta hanyar diflomasiyya, Isra'ila na iya "yaki ta bangarori da yawa, kuma ma suna kan shiri.

Wuta tana ci bayan wani harin roka da aka kai daga Lebanon
Wuta tana ci bayan wani harin roka da aka kai daga Lebanon

Shugaban Amurka Joe Biden ya jinkirta samar da manyan bama-bamai tun cikin watan Mayu saboda damuwar kan kai hari da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Gaza, sai dai a makon da ya gabata gwamnatinsa ta musanta zargin da Netanyahu n ya yi cewa, dakatar da tura makaman ya shafi sufurin wasu kayayyaki.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG