Yayin da shugabanni ke ci gaba da neman hanyar warware matsalar sace-sacen mutane domin kudin fansa, wadda ta addabi arewacin Najeriya, fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmed Gumi, ya ce Fulanin da ake zargi da aikata laifukan ba barayi ba ne.
A karon farko kasar Ghana ta karbi alluran rigakafin coronavirus da ake samarwa ta hanyar shirin raba alluran rigakafi na bai daya a duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke kula da shi.
Ana cigaba da samun bayanan yadda rayuwa take a duniyar sama.
Rahotanni daga jihar Borno na nuna cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun sake kwace garin Marte dake arewacin Borno, tare kwashe makaman jami’an tsaro da kafa tutocinsu.
A kalla mutum hudu ne wasu yan bindiga suka kashe tare da yin awon gaba da wasu mutum 10, a kauyen Akufe na gundumar Kuchi a karamar hukumar Sarkin Pawa a jihar Neja ta Najeriya.
Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), ta ce za ta tura zubi 11,000 na alluran rigakafin cutar Ebola, da kuma kwararru sama da 100 zuwa Guinea, don shawo kan barkewar cutar Ebola a wannan kasa ta Afirka ta Yamma.
A daidai lokacin da ake ci gaba da zama cikin zullumi tare da neman hanyar ceto daliban Kagara da aka sace, wasu daga cikin daliban da suka tsallake rijiya da baya sun bayyana halin da suka shiga
Biyo bayan sace dalibai da malaman makarantar kimiyya ta gwamnati da ke Kagara a jihar Neja, Majalisar Dattawa na kira ga shugaban kasa ya gaggauta ayyana dokar ta baci a fannin ilimi.
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, da su kafa wani kwamitin aiki da cikawa wanda zai tsara tare kuma da tafiyar da aikin rigakafin COVID-19 na bai daya a duniya.
An cigaba da kara samun riga kafin annobar coronavirus.
An samu barkewar annobar Ebola a wasu kauyuka da ke kasar Guinea.
Kalaman gwamnan jihar Benue mai cewa fadar shugaban kasa na rikon sakainar kashi kan irin kashe-kashen da ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa a sassa daban-daban na Najeriya, ya janyo kakkausan martani daga wasu kungiyoyi dake hankoron samar da ci gaban Najeriya.
A daidai lokacin da wasu shugabannin al’umma ke daukar mataki ko kiran a samu da hanyar sasantawa da ‘yan bindiga domin samar da masalaha ga matsalar tsaro, shin ko ‘yan bindigar sun shirya ajiye makamansu?
Hukumar dake sa ido kan kafafen labarai a China, ta ce ta dakatar da kafar labaran BBC daga gudanar da ayyukanta a kasar, saboda abin da ta kira “Saba ka’ida sosai game da batutuwan yadawa a labarai.”
Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci gwamnan babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, don ya yi wa kwamitocin ta bayani game da dakatar da amfani da kudaden yanar gizo na zamani mai suna cryptocurrency.
Gwamnonin arewacin Najeriya sun dukufa wajen neman hadin kan gwamnatin tarayya, don kafa rugage da wuraren kiwo domin hana Fulani yawon kiwo da ke sanadin tashe tashen hankula.
Yau za'a fara sauraron karar sake tsige tsohon shugaban Amurka Donald Trump a majalisar dattawan Amurka.
Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi alkawarin cewa Amurka za ta yi matukar dada taka rawa a harkokin duniya a tsawon wa'adinsa, ya na mai kawo karshen abin da ya kira "shekaru hudu na yin watsi da kuma amfani da harkokin waje ba bisa ka'ida ba" da tsohon Shugaba Donald Trump ya yi.
A kokarin magance matsalar tsaro da garkuwa da mutane don kudin fansa akan tituna, gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin shimfida hanyar Maiduguri zuwa Bama, wadda za ta kai har zuwa wasu kasashen Afirka.
Domin Kari