Masana lamurran tsaro na ganin rashin karfafawa hukumomin tsaro a Najeriya na daga cikin abubuwan da ke kawo koma baya ga yunkurin shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar.
Gobara ta sake afkawa sansanin ‘yan gudun hijira tare da lakume gidaje 83 a garin Maiduguri na jihar Borno. Lamarin da ya jefa ‘yan gudun hijirar cikin mawuyacin hali.
An kaddamar da aikin allurar rigakafin cutar coronavirus a Jamhuriyar Nijar a ranar Talata, allurorin da kamfanonin Astrazeneca da Sinopharm suka samar.
A yanzu mata 8 ake da su a Majalisar Dattawa, sannan 13 a Majalisar Wakilai - adadin da ke nufin kashi 4.4 a cikin 100 kacal ke Majalisar.
Al’umomin kasar Chadi sun fara nuna damuwa a game da yadda hukumomin suka kasa bayyana matsayinsu game da bukatar mika ‘yan tawayen kungiyar Fact ga gwamnatin rikon kwarya, wadda ta fara zargin jamhuriyar Nijar da nuna bangaranci a rikicin da ake yi.
Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa har 33 a jihar Zamfara.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nemi taimakon Amurka wajen yaki da kalubalen tsaro da kasar ke fama da shi.
Rahotanni na nuni da cewa wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari gidan gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, tare a cinnawa gidan wuta.
Hukumomin tsaron Najeriya na ci gaba da kamen mutanen da ake zargi da taimakawa ta’addanci a kasar, baya ga 'yan kasuwar canji da ke tsare a hannunsu tun kusan watai 3 da suka gabata.
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya rasu ranar Talata sakamakon raunin da ya ji a ranar Talata a fagen daga, inda aka kwashi gumurzu tsakanin askarawansa da ‘yan tawayen kungiyar Fact a yankin Arewacin kasar.
Matsalar garkuwa da mutane na kara zama babbar barazana ga mazauna wasu yankunan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Sabon sarkin Alhaji Ahmed Garba Gunna, ya nemi hadin kan al’ummar masarautar wajen shawo kan babbar matsalar da ke ci wa masarautar tuwo a kwarya, wacce ta shafi rashin zaman lafiya.
An haifi sabon mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba a garin Gaidam da ke arewa maso gabashin jihar Yobe a shekarar 1963.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin a kamo a kuma hukunta dukkan 'yan bindigar da suka kai hari a gidan yari na Owerri, babban birnin jihar.
"Sai da na yi gudun sama da kilomita daya da rabi ba tare da na tsaya ba. Ina godiya ga Allah da ya ba ni wannan karfi.” In ji Ortom.
Mayakan Boko Haram sun addabi arewa maso gabashin Najeriya sama da shekaru goma, tare da tilastawa mutum miliyan 2 tserewa daga gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
A daidai lokacin da aka fara yi wa rukunin farko na ma’aikatan kiwon lafiya allurar riga-kafin coronavirus ta AstraZeneca a Najeriya, ana samun mabanbantan ra’ayoyi game da riga-kafin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun karbi alluran farko na riga-kafin coronavirus na kamfanin AstraZeneca.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta lashi takobin kawo karshen zanga zangar da aka shafe kwanki uku ana gudanarwa a birnin Yamai, bayan fitar da sakamakon zaben ranar 21 ga wannan wata.
Gwamnatin jihar Sokoto ta tasa keyar wasu magidanta bakwai zuwa gidan gyara hali, bayan da ta sake gurfanar da su gaban kotu akan zargin yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyade.
Domin Kari