Kasar Nepal na gudanar da zaman makoki a yau Litinin, kwana guda bayan da jirgin saman Yeti Airlines ya yi hatsari dauke da fasinjoji 72 da ma'aikatan jirgin daga Katmandu zuwa garin Pokhara na masu yawon bude ido.
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wani dan kasar Iran kuma dan kasar Birtaniya.
Kwamitin bincike na musamman a jihar Geogia ta Amurka, da ke binciken ko shugaban kasar na wancan lokacin Donald Trump da abokansa sun aikata wani laifi yayin da suke kokarin juya zaben da ya fadi a shekarar 2020 ya kammala aikinsa.
Kamfanin Raya Kasa ta Kamaru CDC ta yi kira ga dubban ma’aikatan gonaki da suka tserewa rikicin yan awaren kasar da su koma bakin aiki.
Bayan kwashe zagaye 15 ana kada kuri'a cikin kwanaki biyar ga dan jam'iyyar Republican mai sausaucin ra’ayi, daga karshe an zabi Kevin McCarthy a matsayin kakakin majalisar wakilan Amurka a yau Asabar.
A daidai lokacin da ake shirye-shiryen jana’aizar Fafaroma Benedict mai ritaya, an bayyana kalaman karshe da ya furta kafin komawarsa ga mahalacci.
Wata kotu a birnin Accra ta tasa keyar wasu yan Najeriya hudu zuwa gidan Yari, kan laifukan hada baki tare da sace wasu mata yan kasar Canada biyu a shekarar 2019.
Yayin da ‘yan Habasha a fadin duniya ke jiran ganin ko yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma, mai sarkakkiya za ta yi aiki, wani gungun ‘yan kasar mazauna kasashen ketare ya hallara a nan hedikwatar Muryar Amurka da ke birnin Washington don tattauwa kan batun.
Yayin da ake ci gaba da yaki da gurbata muhalli, ta hanyar hana sare bishiyoyi a kasar Kamaru, gwamnatin jihar Arewa mai nisa ta gurfanar da mutum 50 gaban kotu kan laifin sare itatuwa.
Kasar Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya bayan ta doke Faransa mai rike da kofin a bugun fenareti da ci 4-2, bayan da suka tashi 3-3 bayan karin lokaci.
Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabinsa ga shugabannin Afirka da suka hallara a birnin Washington, cewa Amurka za ta iya zama babbar hanyar bunkasa nahiyarsu a shekaru masu zuwa.
A lokacin da Amurka da China da kasashen Yamma ke fafatawa a gasar wa yafi kusanci da kasashen Afirka, shugaban kasar Nijar ya danganta nasarar da China ke samu a Afirka da rashin tsoro.
Shugabannin kasashen Afirka sama da 40 sun hadu a birnin Washington DC don halartar wani muhimmIn taro da shugaban Amurka Joe Biden ya shirya karo na farko tun hawansa mulki.
Rundunar Sojin Amurka ta bukaci Najeriya ta da gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin kashe yara a yakin sojojin suke yi da kungiyar Boko Haram.
Domin Kari