Bangarorin da ke fada a Afghanistan sun zargi juna da kaddamar da sabbin hare-hare a kasar, yayin da wakilansu suka yi ganawar tarihi a rana ta biyu a jiya Lahadi a birnin Qatar, ganawar samar da zaman lafiya da Amurka ta shiga tsakani.
A cigaba da takaddamar da ake yi kan labarin cewa kungiyar Boko Haram za ta kutsa cikin Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Hukujmar Kwastan ta nesanta kanta.
Ga dukkan alamu shirin gudanar da zaben kasar Venezuela zai fuskanci cikas ganin yadda jagoran 'yan tawaye ke kiran sojoji su nesanta kansa daga shirin zaben.
Dambarwar siyasar kasar Belarus na dada kazancewa yayin da aka tsare jagoriyar siyasar kasar Belarus.
Yayin da takaddama kan tsarin da ya kamata a yi amfani da shi wajen gyara kundin tsarin mulkin Najeriya ke kara yawa, ra'ayin Kungiyar Dattawan Arewa, ta a yi amfani da kuri'ar raba gardama a maimakon kashe makudan kudi, ya fara samun goyon baya.
“Idan dai kasahe sun shawo kan cutar corona, to bude harkokin yau da kullum ba zai zama matsala ba, amma a bude ba tare da wata takamammiyar nasara ba, shi ne zai janyo babban bala'i.” In ji Tedros
Kalaman uwargidar shugaban Amurka na daren jiya Talata yayin babban taron jam'iyyar Republican sun sha bamban da na mijinta, Shugaba Donald Trump, lamarin da ke ta ba masu nazari mamaki.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International da kungiyar kare hakkin dan adam ta Angola OMUNGA, na zargin jami’an tsaro da kashe akalla mutane bakwai.
An harbe wani mutum har lahira yayin da aka shiga dare na uku a jere na zanga-zanga a garin Kenosha da ke jihar Wisconsin, saboda harbe wani Baƙar fata da 'yan sanda suka yi ranar Lahadi.
A yayinda ake bikin tunawa da ranar Hausa ta duniya a yau Alhamis 26 ga watan Agusta, a Jamhuriyar Nijar kungiyoyin bunkasa harshen Hausa sun shirya wani taron hadin gwiwa da hukumomin kasar da nufin karrama wannan ranar.
Kwamitin ko ta kwana na Shugaban kasar Najeriya da ke sa ido a yaki da cutar Covid-19 ya bayyana cewa sakamakon gwajin da aka yi ya tabbatar da kamuwar mutane 684 da cutar COVID-19 wadanda suka dawo daga kasashen ketare.
Domin Kari