Majalisar addinai ta jihar Filato ta ce za ta dauki matakan tattaunawa a matsayin hanya mai kyau ta zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban a jihar.
Gwamnatin rikon kwarya a kasar Chadi ta yi watsi da dukkan wani tayin sulhu da ‘yan tawayen kungiyar FACT wadanda suka yi ikirarin halaka shugaba Idriss Deby a farkon makon jiya.
Zhao ta lashe kyautar lanbar yabo na Oscar a matsayin babban darakta na "Nomadland," ta kuma zama mace ta biyu kuma mace ta farko da ba farar fata ba da ta lashe kyautar.
A yayin da hukumomin tsaro a Najeriya ke cigaba da tsare ‘yan kasuwan canji da gwal sakamakon zargin su da tallafawa ayyukan ta’adanci, yan uwa da abokan mutanen da ke tsaren na cigaba da kokawa kan rashin sanin halin da ‘yan uwan nasu ke ciki.
Kwana guda da sake sace dalibai a jahar Kaduna, gwamnatin jahar ta ce har yanzu ba wani labari game da adadin daliban da aka sace ko kuma inda aka boye su.
A karshen watan Maris, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sanar da cewa, gwamnatin Amurka ta ware kudi har dala miliyan 30 don hanzarta bada tallafi ga barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Jamhuriyar Guinea.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta samar da kayan aiki don tabbatar da duk wani dan Najeriya ya sami rigakafin COVID.
Masana kula da lafiya a Najeriya sun bayyana bukatar da ke akwai ta amfani da tsarin binciken kiwon lafiya na hadin gwiwa tsakanin likitocin dabbobi da na al'umma domin saukaka gano cuta da maganin ta.
A watan nan na Afrilu aka cika shekaru biyu da munanan hare-haren makamai masu guba a Syria: na farko a ranar 4 ga Afrilu, 2017 lokacin da gwamnatin Assad ta tura makamai masu guba a garin Khan Sheikhoun da ke Idlib; na biyu a ranar 7 ga Afrilu, 2018 akan garin Douma.
A yayin da ake ganin hare-haren 'yan-bindiga sun yi sauki a watan Ramadan, al'umar garuruwan Kuriga da Udawa da kewaye dake karamar hukumar Chukun jahar Kaduna sun ce su hare-haren ma ta'azzara su ka yi a wannan wata na Azumi.
A yayin da hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA ta cika shekara 20 da kafuwa a Najeriya, ‘yan kasar sun fara bayyana mabambantan ra’ayoyinsu game da tasirin ayyukan hukumar a fadin kasar.
China na ci gaba da yakin neman wargaza dimokiradiyya da 'yancin bil adama a Hongkong, kuma masu rajin kare dimokiradiyya na ci gaba da shan wahala saboda goyon bayan 'yancin bil Adama.
Wasu ‘yan bindiga a Jamhuriyar Nijer sun hallaka fararen hula 19 a kauyen Gaigorou da ke karamar hukumar Dessa a jihar Tilabery lamarin da ya tada hankalin jama’a sakamakon lura da yadda ‘yan ta’adda ke farwa fararen hula a ‘yan makonnin nan.
Gwamnatin Najeriya ta ce shirinta na bunkasa fannonin tattalin arziki marasa alaka da bangaren mai, na haifar da sakamako mai kyau ta fuskar habaka tattalin arzikin kasar.
Fadar Shugaban Najeriya ta ba da tabbacin cewa, ba ta manta da 'yan mata daliban Chibok da aka sace a shekarar 2014 ba, tana mai cewa a ko da yaushe, tana tunaninsu kamar yadda iyayensu suke yi.
Gobarar da ta tashi a wata makarantar firamarin birnin Yamai ta haddasa rasuwar dalibai da dama yayin da baki dayan dakunun karatu suka kone kurmus.
Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen kara samarwa mayakan ruwan jiragen ruwan yaki da ma sauran kayayyakin aiki, don kara tunkarar matsalar tsaro gadan gadan.
Domin Kari